IHR na rokon da a tsaurara tsaro a sasanonin maniyyata aikin hajjin Nijeriya



Kungiyar nan mai zaman kanta da ke ba da rahotannin yadda aikin hajji da Umrah ke gudana wato Independent Hajj Reporters, ta yi kira ga gwamnatin tarayyar Nijeriya da ta jihohi da su samar da wadataccen tsaro ga maniyyatan aikin hajjin bana na 2024.

Kiran wannan kungiya na a cikin wata sanarwa daga shugabanta Alhaji Ibrahim Muhammad da DCL Hausa ta samu kwafi, wanda kiran ya zo daidai da lokacin da ake dab da fara jigilar mahajjatan Nijeriya zuwa kasar Saudiyya don sauke farali.

Sanarwar ta ce akwai sama da maniyyatan Nijeriya 65,000 da za su rika barin gidajensu zuwa sansanonin alhazai daban-daban domin tantance su da kuma jigilarsu zuwa filayen jirage kusan 15 cikin kwanaki 30 masu zuwa, don haka ne kungiyar ke kira da babbar murya ga hukumomi na su saka idanu sosai don tabbatar da tsaron rayukan al'umma.

Da kungiyar ta yaba da irin kokarin da hukumomin tsaro suka yi a ayyukan hajji na baya, yanzu haka ma kungiyar ba ta yi kasa a guiwa ba wajen sake tunasar da gwamnatin tarayya da ta jihohi da su sanya jami'an tsaro na musamman da z asu rika sintiri don kare rayukan maniyyatan.

Alhaji Ibrahim Muhammad a cikin sanarwar ya kuma shawarci hukumomin kula da aikin hajji na jihohi da su gargadi maniyyatansu da kada su rika zuwa sansanonin alhazai da tawagar 'yan rakiya da yawa.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp