An kara kudin haya a Abuja, mazauna na ta guna-guni


Rahotannin da DCL Hausa ta samu daga jaridar Daily Trust sun ce an samu karin daga gidan da ake biyan N600,000 yanzu an mayar N850,000 a shekara.

Bayanai dai sun ce yanzu haka mazauna birnin tarayyar na ta guna-gunin wannan karin kudin da aka yi musu.

Kazalika, akwai wanda ake biyan daki daya kan kudi N150,000 yanzu an mayar N250,000 a shekara a Unguwar Dei-Dei. Bugu da kari, akwai wani mazaunin yankin Dutse da ke biyan N550,000 a shekara dakuna biyu wato Two Bed Room, amma yanzu an mayar da kudin sun koma N7000,000.

A yankin Kuje kuwa, akwai gidan da ake biyan N200,000 a shekara, amma yanzu ya koma N280,000 har ma N350,000 a shekara ya danganta da inda gidan yake.

Sai dai da jaridar Daily Trust ta tuntubi masu gidajen hayar, sun shaida cewa matsim tattalin arzikin da Nijeriya ke ciki ne ya sanya su wannan karin, ba da son ransu ba.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp