Shugaba Tinubu ya taya murna ga sabon shugaban kasar Chad


Shugaban Nijeriya Bola Ahmad Tinubu ya taya zababben shugaban kasar Chad Mahamat Idris Deby murna bayan nasarar lashe zaben shugaban kasa da ya yi.

Shugaban na Nijeriya ya hakikance cewa yadda aka gudanar da sahihi kuma ingantaccen zabe a kasar, ya nuna karara yadda al'ummar kasar Chad ke son dimokradiyya ta dore yadda ya kamata.

A cikin wata sanarwa daga mai magana da yawun shugaban kasa Mr Ajuri Ngelale, ta ce Nijeriya za ta yi aiki kafada da kafada da kasar Chad ganin yadda kasashen biyu suke mayar da hankali wajen inganta tsaro da zaman lafiya.

Shugaban kasar ya yi kiran da a cigaba da hadin kai a tsakanin kasashen biyu, sannan ya yi addu'a ga sabon shugaban kasar da ya sauke nauyin al'umma da ke kansa.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp