NAHCON ta aike da ma‘aikatan farko da za su tarbi maniyyata zuwa Saudiyya


Tawagar ma'aikata 43 daga hukumar kula da aikin hajji ta Nijeriya NAHCON za su tashi daga Abuja a gobe Lahadi, zuwa kasar Saudiyya, domin murnar tarbar jirgin farko na mahajjatan Nijeriya a kasar Saudiyya.

Tawagar da ta kunshi jami’an hukumar NAHCON 35 da ma’aikatan lafiya 8 za su je kasar Saudiyya domin shirin karshe na karbar mahajjatan Nijeriya daga jihar Kebbi da za su isa Saudiyya a ranar Laraba 15 ga watan Mayu domin gudanar da aikin Hajjin bana na shekarar 2024.

Da yake jawabi ga tawagar a wani dan takaitaccen biki na ban kwana da aka gudanar a dakin taro na hukumar, Abuja, shugaban hukumar Malam Jalal Ahmad Arabi ya gargadin cewa hukumar za ta dauki tsattsauran mataki a kan duk wanda aka samu rahoton ya kauce wa ka’idar aiki ga amanar da aka dora musu.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp