Shugabannin jam'iyyar APC na mazabar Galadima a karamar hukumar Gusau jihar Zamfara sun sanar da dakatar da shugaban jam'iyyar na jihar Tukur Danfulani.
16 daga cikin 27 na jiga-jigan jam'iyyar a mazabar ne suka sanya hannu kan takardar dakatarwar, inda suka alakanta hakan da rashin shugabanci nagari da suke zargin shi Danfulani da yi.
Sannan su na zarginsa da haddasa rudani da rarrabuwar kai a tsakanin 'ya'yan jam'iyyar