Mu tunkari matsalolin mu kada mubari sufi karfin mu-sarkin musulmi

Mu tunkari matsalolin mu kada mubari sufi karfin mu-sarkin musulmi

Maimartaba Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar, ya shawarci ‘yan Nijeriya da su amince da kalubalen da suke fuskanta, su kuma yi kokarin magance su.

Sarkin ya bayyana haka ne yayin da yake karbar bakuncin ministan tsaro, Muhammad Badaru Abubakar a fadarsa a ranar Juma’a, sarkin yace bai kamata mubari wasu suyi nasara a kan mu ba,domin idan babu tsaro, ba za mu iya samun komai ba.


Ya ce ministan tsaro ya san nauyin da Allah ya dora masa,kuma ya yi imanin yana tuntuɓar masu ruwa da tsaki don taimaka masa wajen yaki da matsalar tsaro a fadin kasar nan.


Akwai kalu bale, amma masu ruwa da tsaki koda yaushe suna tuntubar juna domin samun mafita a al'amura da dama da suka shafi harkokin tsaro.


Sarkin Musulmi ya bada tabbacin cewa sarakunan gargajiya za su yi duk mai yiwuwa don ganin an samu zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar nan.


Sai dai ya yi kira da a ci gaba da tallafa wa jami’an tsaron da su ka sadaukar da rayuwarsu domin zaman lafiya a kasar nan.

Post a Comment

Previous Post Next Post