'Yan Nijeriya milyan 4.8 na iya fama da karancin abinci a ban in ji majalisar dinkin duniya


Majalisar Dinkin Duniya UN ta yi hasashen cewa da yiwuwar mutane milyan 4.8 a Nijeriya su yi fama da matsanancin karancin abinci a shekarar nan ta 2024.

Bugu da kari, majalisar dinkin duniyar ta ce a kwai yara kanana milyan 5.9 a Nijeriya da ke fama da matsanancin karancin abinci.

Adadin kamar yadda Mohammed Fall, babban mai kula da ayyukan majalisar a Nijeriya ya ce, shi ne mafi girma a duk fadin duniya.

Ya ce akwai yara kanana 'yan kasa da shekaru 5 su 700,000 da ke fama da karancin abinci da kuma wanda bai gina jiki a jihohin Borno, Adamawa da Yobe.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp