Sojoji na zafafa hare-hare kan 'yan bindiga a jihar Zamfara

Gwamna Dauda Lawal ya yaba wa rundunar hadin guiwa kan sabbin hare-haren matsin lamba kan ‘yan bindiga a jihar Zamfara.

A karshen makon da ya gabata ne rundunar soji ta kara tura wasu dakarun sojoji zuwa Zamfara a kokarin da suke yi na dakile ayyukan ‘yan bindiga a yankunan da ke fama da rikici a jihar.

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ta bayyana aikin samar da tsaro da sojoji ke ci gaba da yi a matsayin matakin da ya dace na dakile ayyukan ‘yan bindiga a Zamfara.

Sanarwar ta kuma jajanta wa al’ummomin da hare-haren ‘yan bindiga ya shafa a baya-bayan nan, tare da ba da tabbacin ci gaba da goyon bayan gwamnatin jihar ga sojojin da ke fagen daga.

Sanarwar ta kara da cewa: “Ayyukan da sojoji ke ci gaba da yi a yankunan da ke fama da karancin tsaro a Zamfara abin yabawa ne matuka, musamman idan aka yi la’akari da nasarorin da aka samu tun fara kai hare-hare a karshen makon da ya gabata.

“Aikin ya haifar da gagarumar nasara a kananan hukumomin Bungudu, Tsafe, Maru, da Zurmi, wanda ya yi sanadiyyar kisan jagoran ‘yan bindiga, Abu Dan Dunkwuifa, wanda ya shahara da ta’addanci a kauyukan Bungudu da Maru.

“A Magama Mai Rake da ke yankin Dansadau a karamar hukumar Maru, sojojin sun yi nasarar kashe ‘yan bindiga da dama.

“Harin da sojoji suka sake kai wa a Nasarawar Burkullu a karamar hukumar Bukkuyum ya yi sanadiyar ceto mutane da dama da aka yi garkuwa da su a kauyukan Kamaru, Tungar Rogo, da Matsare, tare da kwato shanu da dama da aka sace.

“Jita-jitar cewa an yi garkuwa da mutane sama da 500 ba gaskiya ba ne kuma wasu mutane ne da ba sa son zaman lafiya ya dawo a jihar Zamfara.

Gwamnan ya kuma jajanta wa al’ummar da ‘yan bindiga suka kai wa hari a jihar.

“Gwamnatin jihar Zamfara na son nuna juyayi ga al’ummomin da ‘yan bindiga suka kai wa hari kwanan nan. Mun himmatu sosai wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama'a.

"Gwamnatinmu za ta ci gaba da tallafa wa sojojin da ke yaki da rashin tsaro tare da bayar da duk wani tallafin gaggawa ga wadanda rikicin 'yan bindiga ya shafa a jihar."

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp