'Yan siyasa suna raba kuɗin da suka sãta da 'yan ƙasar.


Babban mai tsawatar wa na majalisar Dattawan Najeriya sanata Ali Ndume yayi zagin cewa 'yan Najeriya ne ke tunzura 'yan siyasar ƙasar yin almundahana da kuɗin ƙasar, saboda haka bai kamata su fuskanci wani hukunci ba.

Sanata Ndume ya nuna cewa idan aka kwatanta almundahana da 'yan siyasa ke yi bai yi kusa da na wasu ba, yana mai cewa idan 'yan siyasa basu raba kuɗi ba TOH tabbas baza su sake komawa kujerar da su ke riƙe da ita ba.

Ndume ya baiyana cewa idan ma za'a yanke hukuncin kisa ga masu laifin satar kuɗin gwamnati, bai kamata ace an kashe wanda ya saci Naira miliyan daya ko biliyan ɗaya ba, Wanda kamata a kashe shi ne wanda aka samu da laifin satar kuɗin gwamnati da ya kai Naira tiriliyan ɗaya.

Sanatan ya goyi bayan hukuncin kisa kuma ga masu safarar miyagun kwayoyi wadanda a cewar sa su suka fi cancanta da hukuncin kisa.

Post a Comment

Previous Post Next Post