Bai halatta gwamnati ta yi amfani da kuɗin fansho Naira tiriliyan 20 ba - Atiku


Tsohon mataimakin shugaban Najeriya kuma ɗan takara na babbar jami'ya mai adawa PDP Atiku Abubakar ya zargi gwamnatin shugaba Tinubu da yunkurin sake tafka wani almundahana ta anfani da Naira tiriliyan 20 na Fansho ta yi wasu ayyuka na daban.

Atiku ya ce wannan yunkuri na gwamnatin Tinubu abu ne mai matuƙar hadari, wadda kan iya haifar da matsanancin yanayi ga  'yan Najeriya waɗanda suka daɗe suna tãra kuɗin su na fansho domin su dogara da shi bayan yin ritaya daga aiki.

Atiku Abubakar ya ce maimakon yin hakan, kamata yayi gwamnatin ta Tinubu ta nemo masu saka jari dan gudanar ayyukan samar da kayakin more rayuwa da take ƙokarin yin amfani da kuɗin 'yan fansho wurin aiwatar da su.

Gwamnatin taraiya ta bakin ministan tattalin arziki da na kudi ta sanar da wani sabon tsari na amfani da kuɗaɗen fansho da wasu kuɗaɗe wurin samar da kayan more rayuwa a Najeriya.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp