Shin me ke kunshe a cikin farashin abinci na wannan makon?

Manoman masara na ci gaba da darawa ganin yadda take daraja a kasuwa, domin kuwa a wannan makon an sayar da buhunta mai cin tiya 40 kan kudi Naira N70,000 a kasuwar Mile 12 International Market Lagos da ke kudancin Nijeriya, a makon jiya aka sayar kan kudi N67,000, cikin kwanaki bakwai ta kara Naira dubu uku kenan. 

Amma a abin zas-sauki a jihar Adamawa, inda ake saidawa kan kudi Naira 52,000, amma a makon jiya an sayar da buhun masarar mai cin tiya 40 aka sayar kan kudi Naira N56-58, wato dai a wannan makon an samu saukin kusan Naira N4,000-6,000.

Can kuwa kasuwar Dawanau jihar Kano, Naira dubu N65,000 ake sayar da buhun masarar a wannan makon, a yayin da kasuwar Giwa jihar Kaduna ake sayarwa kan kudi N62,000, sai dai a makon jiya an sayar da masarar N59,000, ta kara N3,000. Sai a kasuwar Mai'adua jihar Katsina ake sayar da buhun masarar mai cin tiya 40 kan kudi Naira N67,000 a yayin da a makon jiya aka sayar da masarar a Mai'adua jihar Katsina N64,000.

Ta bangaren shinkafar waje kuwa, a makon jiya an sayar da ita kan kuɗi N71,000 a kasuwar Mile 12 International Market Lagos, amma a wannan makon ta kara N7000 wato yanzu ta koma N78,000. A kasuwar Dawanau jihar Kano kuwa shinkafar baturen ta kama N80,000 daidai a wannan makon, amma a makon jiya an sayar kan kudi Naira N75,000, ta kara Naira dubu N5000 kenan. 

A kasuwar Mai'adua jihar Katsina kuwa a makon jiya, an sayar da shinkafar wajen N68-69,000, amma a wannan makon ake sayarwa kan kudi Naira 73,500, nan din ma dai ta kara kudi.

Ita kuwa shinkafar 'yar Hausa da aka fi sani da Jamila, N130,000 buhunta yake a kasuwannin Mile 12 International Market Lagos da Dawanau jihar Kano da Kasuwar Gombi jihar Adamawa a wannan makon, sai dai a kasuwar Mai'adua jihar Katsina ana sayarwa kan kudi Naira N125,000, a yayin da kasuwar Giwa jihar Kaduna ake sayar da buhun jamilar N128,000 duk a wannan makon.

Amma a makon jiya, an sayar da buhun shinkafar Hausa din kan kudi Naira N142,000 a kasuwar Mile 12 International Market Lagos, sauran kasuwannin kuwa, yadda aka sayar makon jiya, haka aka sayar wannan makon.

Ta bangaren masu kosai da alale kuwa, ana sayar da buhunsa a kasuwar Mile 12 International Market Lagos kan kudi Niara N135,000 a wannan makon, N125,000 kuwa a kasuwar Dawanau jihar Kano, sai ake sayar da buhun waken kan kudi Naira 130,000 a kasuwar Gombi jihar Adamawa. Ita kuwa kasuwar Mai'adua jihar Katsina na sayar da buhun waken N112,000, kasuwar Giwa jihar Kaduna kuwa ake sayar da buhun wake farin da ake garo-garo, kosai, da alale kan kudi N110,000. Amma a makon jiya an sayar da buhun wake farin kan kudi N130,000, kasuwar Dawanau jihar Kano kuwa aka sayar a makon jiya kan kudi N113,000-120,000, sai a kasuwar Mai'adua jihar aka sayar da wajen kan kudi N117,000.

Ta fuskar taliyar Spaghetti kuwa a makon jiya, an sayar da ita kan kuɗi N14,500, aka sayar N14,000 a kasuwar Giwa jihar Kaduna sai aka sayar N13,500 a kasuwar Mile 12 International Market Lagos, a Dawanau jihar kuwa a makon jiya an sayar da kwalin taliyar N13,000. Amma a wannan makon an sayar da katan din taliyar kan kudi Naira 14,000 a kasuwar Mile 12 International Market Lagos, a kasuwar Dawanau jihar Kano kuwa ana sayarwa kan kudi N15,500, sai kasuwar Gombi jihar Adamawa ake sayar da taliyar kan kudi N12,800. N16,000 ake sayar da katan din taliyar Spaghetti a kasuwar Mai'adua jihar Katsina a wannan makon, amma a kasuwar Giwa jihar Kaduna ana sayarwa a kan kudi Naira 14,000 cif-cif.


DCL Hausa
Abdullahi Garba Jani

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp