Tinubu ya amince da biyan bashin kudin wutar lantarki N3.3tn.

Tinubu ya amince da biyan bashin kudin wutar lantarki N3.3tn.

Shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da biyan basussukan da ake bin bangaren wutar lantarki a hankali a kan Naira N3.3tn.


Gwamnatin tarayya ta ce hakan na daga cikin matakan da za ta dauka na shawo kan matsalar rashin wutar lantarki a fadin kasar.


Haka zalika, kimanin N1.3tn da ake bin kamfanonin samar da wutar lantarki da kuma gwamnatin tarayyar za ta biya ne ta hanyar tsabar kudin da ta ayyana.


Tuni dai gwamnatin tarayya ta fara biyan kudaden kashi na bashin N1.3tn da ake bin ta sannan ta kammala shirin biyan kashi na biyu ta hanyar takardar sheda a cikin wa'adin shekaru biyu zuwa biyar masu zuwa.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp