An janye dakatarwar da aka yi wa shugaban jam'iyyar APC na jihar Zamfara Tukur Dan Fulani.

An janye dakatarwar da aka yi wa shugaban jam'iyyar APC na jihar Zamfara Tukur Dan Fulani.

Shugabannin jam’iyyar APC na unguwar Galadima da ke Gusau a jihar zamfara sun janye dakatarwar da suka yi wa shugaban jam’iyyar APC na jihar, Alhaji Tukur Dafulani.


Da yake zantawa da manema labarai a Gusau, shugaban jam'iyyar na Unguwar  Galadima, Alhaji Sani Ibrahim, ya ce an janye dakatarwar ne bayan wani taron sulhu da aka yi da wasu ‘ya’yan jam’iyyar.


Ya ce wasu ’ya’yan Unguwar da suka shiga cikin dakatar da shugaban jam’iyyar, sun shiga ciki ne domin kawo rudani a jam'iyyar.


Haza zalika, shugaban jam’iyyar APC na karamar hukumar Gusau, Abubakar Tijjani Dan’Aya, ya yabawa mambobin jam’iyyar da suka koka tare da kawo daidaito kan janye dakatarwar da suka yi wa shugaban jam’iyyar.

Post a Comment

Previous Post Next Post