Zan ci gaba da tsayawa takarar shugaban kasa,muddin Ina raye-Atiku Abubakar

 Zan ci gaba da tsayawa takarar shugaban kasa,muddin Ina raye-Atiku AbubakarDan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a 2023, Atiku Abubakar, ya sha alwashin ci gaba da tsayawa takara muddin yana cikin koshin lafiya.

Atiku ya bayyana haka ne lokacin da yake hira da sashen hausa na Muryar Amurka a Abuja.

Da yake tsokaci kan rikicin da ke faruwa a jam’iyyarsa ta PDP, ya ce akwai bukatar jam’iyyar ta hada kai tare da kulla kawance da sauran kungiyoyin siyasa domin lashe zaben shugaban kasa a 2027 mai zuwa.

A cikin hirar ta sa Atiku ya ce: tabbas zai ci gaba da tsayawa takara muddin yana da rai da lafiya.

Yace ko da tsohon shugaban Amurka Abraham Lincoln ya yi takara sau bakwai kafin daga bisani ya yi nasara.

To sai dai idan aka yi la’akari da halin da jam’iyyar PDP ke ciki a halin yanzu, a bayyane yake cewa yunkurin hannu daya ba zai wadatar ba wajen lashe zaben. Ana buƙatar goyon baya mai ƙarfi da haɗin gwiwa tare da sauran jam'iyyu.

Post a Comment

Previous Post Next Post