Jami'an DSS sun musanta kutsawa fadar Sarkin Kano

 Jami'an DSS sun musanta kutsawa fadar Sarkin Kano 


Hukumar tsaron DSS ta musanta mamaye fadar Sarkin Kano, kamar yadda daraktan hukumar a Kano Muhammad Alhassan ya shaida wa manema labarai.


Muhammad Alhassan ya ce sun aike da jami'ansu ne don tarbar uwargidan shugaban kasa Sanata Oluremu Tinubu da za ta ziyarci fadar.


Amma dai ya ce tuni sun janye jami'an nasu biyo bayan samun labarin cewa an dage zuwan uwargidan shugaban kasar, bayan samun labarin cewa Sarkin ba ya gari.

Post a Comment

Previous Post Next Post