Ya kamata a yi wa Tinubu uzuri, Nijeriya ba za ta gyaru a dare daya ba - Sarkin Kano Sanusi


Sabon Sarkin Kano Muhammad Sanusi 2, ya ce akwai bukatar 'yan Nijeriya su fuskanci gaskiya kada a rude su, domin kuwa shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ba zai iya magance tarin matsalolin da Nijeriya ke fama da su ba cikin shekara daya.

Sabon Sarkin na Kano ya yi wannan jawabin ne a Port Harcourt babban birnin jihar Rivers.

Duk da dai 'yan Nijeriyar na fuskantar kalubale iri-iri, tun ma kafin a rantsar da shugaba Tinubu a Mayun shekarar bara, amma sanarwar cire tallafin man fetur da shugaban kasar ya yi a yayin jawabinsa na karbar mulki ya sa mutane da yawa sun kara fadawa cikin mawuyacin hali ta dalilin tashin farashin kayan abinci da sauran kayan masarufi.

Har yanzu dai a iya cewa ba a fara gani a kasa ba na tallafin da gwamnatin tarayya da ta jihohi ke cewa su na badawa don rage radadin cire wannan tallafin man fetur.

Sai dai tsohon Gwamnan babban bankin Nijeriya CBN, Muhammad Sanusi, ya ce wadannan matakai da shugaba Tinubu ya dauka sun zama wajibi.

Ya ce ya zama dole a fada wa juna gaskiya komai dacinta, domin kuwa matakan da Shugaba Tinubu ya dauka, su ne hanya mai bulle wa Nijeriya.

Muhammad Sanusi ya ce irin rikon sakainar kashin da aka yi wa Nijeriya cikin shekaru 10, ba zai yiwu a iya gyarawa cikin watanni kasa da 10 ba. Ya kara da cewa za a ga mafiyawan alfanun wadannan matakai a nan gaba, amma sai an kai zuciya nesa.

Sarki Muhammad Sanusi dai da ya ke kusan na hannun damar shugaba Tinubu, tuni yana da raayin a cire tallafin man fetur muddin ana so a farfado da tattalin arzikin kasa.

Ya yi fatar cewa wannan wahala da wasu 'yan Nijeriya ke sha, za ta zamo takaitacciya.

Post a Comment

Previous Post Next Post