Ana yunkurin mayar da Aminu Ado Bayero bisa karagarsa a Kano

Ana zargin dawo da Aminu Ado Bayero cikin Masarautar Kano da sanyin safiyar Asabar din nan bayan tube rawaninsa da aka yi aka mayar wa da Muhammad Sanusi

Wata majiya daga filin jirgin sama na Malam Aminu Kano ta shaida wa jaridar Daily Nigerian cewa an jibge jami'an tsaro masu tarin yawa da za su tsare lafiyar tsohon Sarkin na Kano Aminu Ado Bayero  a fadar sarkin Kano da aka kudiri aniyar mayar da shi.

Jaridar ta wallafa cewa shi ma sabon Sarkin na Kano Muhammd Sanusi ya yi gaggawa tarewa a fadar don dakile yunkurin dawo da tsohon sarki Aminu. Ana dai zargin Gwamnatin tarayya da hannu a kitsa kokarin dawo da tsohon sarki Aminu kamar yadda Daily Nigerian ta ba da labari.

Post a Comment

Previous Post Next Post