Mun gano wasu na kokarin tayar da tarzoma a kano-CP Gumel.

Mun gano wasu na kokarin tayar da tarzoma a kano-CP Gumel.

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ce ta gano wani shiri na tayar da tarzo ma a jihar kan rikicin masarauta.


Kwamishinan ‘yan sandan Kano,CP Mohammed Usaini Gumel ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a daren Litinin .


Gumel ya ce gwamnatin jihar ta na kokarin daidaita batun masarauta kuma duk wani rashin jituwa ana sa ran za a warware shi a kotu ga duk wanda yake da korafi.


Yace mu a matsayinmu na jami’an tsaro muna tsayawa kan doka kuma za mu aiwatar da ita.


Ya kara da cewa sun samu sahihan bayanai game da bata gari da ke kokarin tayar da tarzoma a wurare, musamman Majalisar Dokoki da sauran muhimman wurare a cikin Jihar, majiyoyi da yawa sun tabbatar da hakan.


Duk wanda ke son ta da tarzoma, jami'an tsaro suna da karfin da za su iya dashi. Mun kammala shirye-shiryen fara sintiri sossai da gano wuraren da aka sanar da mu cewa miyagun na wajen.

Post a Comment

Previous Post Next Post