Mataimakin gwamnan Kano ya janye zargin da ya yiwa Nuhu Ribadu.

Mataimakin gwamnan Kano ya janye zargin da ya yiwa Nuhu Ribadu.

Mataimakin gwamnan Kano, Aminu Abdussalam Gwarzo, ya janye zargin da ya ke yi wa Nuhu Ribadu,mai ba da shawara kan harkokin tsaro kan rikicin masarautar Kano.


Gwarzo ya yi zargin cewa Ribadu ne ya sa aka dawo da Aminu Bayero, wanda aka tube daga sarautar Kano, ta hanyar ba shi jiragen sama guda biyu masu zaman kansu tare da rakiyar jami'an tsaro.


Bayan dawo da Muhammadu Sanusi II,kan karagar mulki,Aminu Ado Bayero ya koma masarautar ranar Asabar,inda ya koma gidan sarki na nassarawa a Jihar.


Gwarzo yace batun cewa an rako tsohon sarki Aminu Ado da jirage biyu tare da rakiyar jami'an tsaro da sukai zargi basu fahimci batun daidai ba.


Sai dai a wata wasika da ya musanta zargin ta hannun lauyoyinsa, Aliyu & Musa Chambers, Ribadu ya bukaci mataimakin gwamnan da ya nemi afuwa.


Wasikar tace wanda suke karewa tare da ofishinsa sun dauki abin da mahimmanci dan haka suna bukatar abasu cikakkiyar hujja akan zargin.

Post a Comment

Previous Post Next Post