Jirgin farko na alhazan Kano ya tashi zuwa kasa mai tsarki.

Jirgin farko na alhazan Kano ya tashi zuwa kasa mai tsarki.

Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da jirgin farko na alhazan jihar Kano domin zuwa kasa mai tsarki dan gudanar da aikin hajjin bana.


Solace Base ta rawaito cewa, jirgin ya tashi da misalin karfe 11:41 na safiyar ranar litinin, tare da adadin mahajjata 578 a cikin jirgin Max Air B747 da ma'aikatansa 20, wanda ya nufi filin jirgin sama na Sarki Abdul-Aziz da ke Jeddah.


Gwamna Abba Kabir ya bukaci maniyyatan da su kasance jakadu nagari na jihar da ma Nijeriya a kasa mai tsarki tare da yi wa jihar da kasa baki daya addu’a.


A nasa bangaren, Darakta Janar na Hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano, Alhaji Lamin Rabi’u Danbappa ya ce mahajjatan da ke cikin jirgin sun fito ne daga kananan hukumomi hudu na jihar da suka hada da Gwale,Dala,Fagge da kuma Ungoggo.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp