Tinubu ya koka da halin da kananan hukumomi ke ciki a Nijeriya.

Tinubu ya koka da halin da kananan hukumomi ke ciki a Nijeriya.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nuna damuwarsa kan tabarbarewar harkokin kananan hukumomin kasar nan, yana mai alakanta hakan da koma bayan ci gaba da kuma kasa shawo kan matsalolin tsaro da suka addabi kasa.


Da yake jawabi a wajen wani taron kasa na kwana guda kan kalubalen tsaro a Nijeriya da kuma shugabanci nagari a matakin kananan hukumomi, shugaban ya jaddada cewa shugabanci nagari a dukkan matakai na da matukar muhimmanci wajen samar da ci gaba da rage rikice-rikice a tsakanin al'umma.


Shugaban wanda ya samu wakilcin Ministan tsaro,Badaru Abubakar, ya ce jihar da ke da kyakkyawan shugabanci ta fi dacewa da magance matsalolin cikin gida kamar yaki da bata gari, tada kayar baya, da rikicin kabilanci da sauransu.


Haka zalika ya ce rashin shugabanci nagari yana haifar da cin hanci da rashawa, rashin zaman lafiya, siyasa, rashin daidaiton tattalin arziki, da kuma tashe-tashen hankula a cikin al'umma wanda ba wai kawai na gurgunta tsaron lafiyar al'umma ta hanyar hana mutane bukatun su na yau da kullun, har ma babbar barazana ce ga tsaron kasa ta hanyar samar da yanayi maikyau ga 'yan kasa.

Post a Comment

Previous Post Next Post