'Yan sanda sun kama 'yan fashi da makami da karin masu aikata laifuka daban-daban a Katsina


Rundunar 'yan sandan jihar Katsina ta ce ta yi nasarar kama mutane 22 da ake zargi da aikata fashi da makami da karin wasu mutane 36 da su ma ake zargi da aikata fyade da luwadi a jihar.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar ASP Aliyu Abubakar Sadiq a taron manema labarai a Katsina, inda ya fadi wasu nasarorin da rundunar ta samu a cikin watan Afrilu da ya gabata.

Kakakin rundunar 'yan sandan ya ce sun kuma yi nasarar kama mutane 10 da ake zargi da hannu a wajen kisan kai. Sannan ya kara da cewa rundunar 'yan sandan ta samu koke-koke 81 na aikata manyan laifuka da suka hada da kisan kai, fashi da makami, fyade da luwadi da satar shanu.

Ya ce cikin watan Afrilu da ya gabata, rundunar 'yan sandan jihar ta yi nasarar kai koke-koke 49 a gaban kotu da aka kama mutane 145 da ake zargi da hannu cikin wadannan batutuwa.

Rundunar 'yan sandan ta ce ta kuma yi nasarar hallaka mutane 12 da ake zargin 'yan bindiga ne ta kuma ceto mutane 30 da aka sace ta kuma kwato dabbobi 492.

Kakakin rundunar 'yan sandan ASP Aliyu Abubakar Sadiq ya ce a cikin wannan wata na Mayu kuwa, rundunar 'yan sandan ta yi nasarar dakile wani yunkurin garkuwa da mutane da 'yan bindiga suka tare wasu motocin haya biyu a kan hanyar Gusau-Funtua, inda ta ceto fasinjoji 52.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp