Marigayi Umaru Musa Yar'adua: Shi ake so ko halinsa....?

 Tunawa Marigayi Shugaba Ummaru Musa 'Yar'adua  

Tun daga ranar 5th ga Watan Mayu na 2010,da Ajaliyar Malam Ummaru Musa 'Yar'adua ta yi,tun daga jajibirin ranar wasu al'ummar Kasar nan ba tare da la'akari da bambamcin Bangare ko Yare ko Akida ko Siyasa ba, a Kasarnan baki daya sukan yi alhini don tunawa da Marigayi Shugaban Kasar Nijeriya Malam Ummaru Musa 'Yar'adua.

 Wannan kuma bai rasa nasaba da ribarsa da aka ci a lokacin rayuwarsa da kuma jagoranci abin misali

Sai dai al'ummar Jahar Katsina ita zata fi karda dalilai dadama na tunawa da wannan Shugaba da ya rigayemu gidan gaskiya Shekaru <14> kenan a bana.

Yakubu Lawal

Musamman wasu Makusantansa na Siyasa suke jagorantar tarukan lakcha da na addu'o'in samun rahmar Ubangiji garesa

A wannan Shekarar abin da ya kara ankarar da al'umma a kan Marigayi Malam Ummaru Musa 'Yar'adua ya cika Shekaru <14> da rasuwa shi ne taron manema labaru da wata Kungiya Mai suna Plesant Library and Book Club dake gaba-gaba wajen dabbaqa tarukan ta yi,tare kara fito da wasu batutuwa da za su iya amfanar duk mai muradin yin mulki a duniya,musamman a wannan lokaci da mafi rinjayen al'umma ke da bukatar kamanci ko madadi

An yi taron kamar yarda aka saba,tare da sa albarkar Shehunnan Malamai na Addini da na Siyasa da Shugabanni da Sarakuna da masu rike da Mukamai da dabam-dabam a matakai dabam-dabam. 

Gwamnan Jahar Katsina Mai ci yanzu mukarrabansa da Tsohon Gwamnan Jahar Katsina a shekaru <8> da suka gabata dama sauran wadanda suka maganta a bagiren sun yi tarayya a kan cewa Malam Ummaru Musa 'Yar'adua Mutum ne MAI GUDUN DUNIYA DA YA SHINFIDA ADALCI NA SHUGABANCIN DA BAI DAMU DA ABIN DUNIYA BA,KUMA KOYI DA SHI MAFITA CE GA MAI SON YA FITA

Tabbas! Dukkan wadanda suka yi wannan shedar ga wannan Shugaba da ya kaura Shekaru <14> da suka shude,sun yi tarayya ce ta kut da kut da shi,musamman a lokacin da ya gwamnatanci Jahar Katsina daga 1999- 2007 da kuma gajeran lokacin da ya mulki Kasar nan ta Nijeriya. 

Bawai a tsakanin Shugabanni ba kadai, ko a bakin talakawan da Malam Ummaru 'Yar'adua ya mulka,fatan dacewa a lahira suke masa,duk da Shekarun da ya zamaninsa, akwai shugabancin da aka ratso bayansa dadama.

Duk da cewar, a baya-bayan nan, a matakai na Jaha da Kasa, Malam Ummaru 'Yar'adua shi ne Shugaba da ya rigayemu, ba a samu wanda ake fadin khairinsa ba zucci da baki kamarsa

Wannan ne ya sanya Maudu'in wannan rubutu ya karkata kan SHIN? SHI AKE SO KO HALINSA....?

Dalilin wannan Maudu'i shi ne Izma'in ra'ayoyi mabambamta sun nuna dole akwai dalili dayan-biyu da ya sa sunan Marigayi Shugaban bai kwaranye ba,kamar wasu na kafinsa da bayansa dama wasu dake raye,amman tauraronsu ya dishe koma ya bace kamar an yi khusufi.

Da ni da duk wanda ya bibiyi yarda taron addu'ar tunawa da wannan Shugaba ya gudana a wannan Shekarar zai lura da karuwar shigar masu fada-aji a fagen mulki da Siyasa dama masu tunanin nan, na kowar tuna bara bai ji dadin bana ba,ta fuskar canjin rayuwa.

Taken da aka yi wa Kundin da aka gabatar wato 'Abinda 'Yar'adua ya fada mani,kuma koyar dani' wanda daya daga cikin yaransa na Siyasa a Katsina, Dr. Muttaqa Rabe Darma ya wallafa na bukatar duk wanda ya ci karo da wannan rubutu ya yi nazari kafin zagayowar irin wannan rana badi. 

Sannan mu tambaya kammu...

SHI muke So ko HALINSA ?

   Alkalamin:

 Yakubu Lawal
 Dan Jarida 
Jami'in Hulda da Jama'a

Post a Comment

Previous Post Next Post