Gwamnatin kasar Benin ta hana lodar danyen man Nijar a ƙasar


Shugaban kasar Bénin Patrice Talon ya tabbatar wa duniya da matakin sa na hana lodar danyen man Nijar daga tashar jirgin ruwan kasar sa zuwa kasuwannin duniya

Shugaba Talon ya kuma nuna takaicinsa kan hawa dokin naki da hukumomin mulkin sojan Nijar suka yi na kin bude iyakar su da Bénin domin kuwa duk kokarin sa na neman samo masalaha a tsakanin kasashen biyu ya citura domin kasa samun gamsasshiyar amsa daga hukumomin na birnin Yamai sakamakon cewa har da ministan harkokin wajen shi ya tura wa mahukuntan na Yamai amma shiru

To amma ya ce a shirye yake ko a yanzu idan mahukuntan na Yamai suka amince suka bude iyakar su ya bar jiragen da suka zo domin daukar danyen man su dauka don ya ce yana fatan daidaituwar al'amura a tsakanin kasashen biyu aminan juna kuma 'yan uwan juna

Post a Comment

Previous Post Next Post