Farashin kayan abinci na wannan makon a kasuwar Dawanau da ke jihar Kano, an saida buhun Masara N60,000 daidai a makon nan, bayan da makon da ya gabata aka sayar N58,000.
Masarar ta fi tsada a kasuwar Mile 12 International Market da ke jihar Legas, da aka saya N67,000, yayin da a makon da ya shude aka saya N65,000 an samu karin dubu 2000 kenan.
A kasuwar Mai'adua jihar Katsina, an sayar da buhun N64,000 a wannan satin, inda a makon da ya gabata aka sayar kan kuɗi N62,000.
Sai kasuwar Giwa da ke jihar Kaduna da aka sai da buhun masara kan kudi ₦59,000 a makon nan, amma a makon jiya N57,000 aka sai da buhun.
To a kasuwar Gombi da ke jihar Adamawa masarar ta ɗan sauka, an sayi buhun N56-58,000 a makon nan, bayan da a makon da ya wuce aka sayar N57-60,000 cif.
Masarar ta fi sauki a kasuwar Gombi da ke jihar Adamawa a arewa maso gabashin Nijeriya da aka saya N55,000 a makon da ke dab da ƙarewa, bayan da a makon da ya shude aka saida N57-60,000.
Idan muka je ga batun Shinkafar Hausa kuwa ta fi sauki a kasuwar Dawanau a da ke jihar Kano a makon nan, an sayi buhun Shinkafar Hausa N122,000, sai dai a makon jiya N118,000 aka sayar da buhun.
Sai dai fa, batun ya sha banban da kasuwar Mile 12 International Market Legos da aka sayar da buhun N142,000 a wannan makon, inda makon da ya gabata aka sayar N120,000 an samun karin kudi har N20,000 daidai a makon guda.
Sai kuma kasuwar Giwa da ke jihar Kaduna da ke biye mata, inda aka sayar da buhun shinkafar Hausa N125,000, amma a makon jiya N120,000 ake sai da buhun, an samu karin N5000 kenan a makon guda kacal.
Shinkafar ta ɗan haure a kasuwar Girie da ke jihar Adamawa a wannan makon, da aka sayar N130,000, sai dai a makon da ya gabata kuwa an sai da N110,000, an samu karin N20,000 kenan a makon nan.
To a kasuwar Kashere da ke karamar hukumar Akko a jihar Gombe kuwa kuɗin buhun Shinkafar Hausa bai sauya zani ba, inda aka sayi buhun N120-130,000, a makon da ya gabata, haka nan aka sai da a makon nan.
An sayi buhun Shinkafar Hausa N130,000 daidai a wannan makon, yayin da a makon jiya aka sayar N120,000 a kasuwar Mai'adua a jihar Katsina.
To a bangaren Shinkafar waje kuwa an sai da buhun kan kuɗi N75,000 a kasuwar Dawanau da ke jihar Kano a makon nan, inda a makon jiya aka sai da N71,000.
A Mai'adua jihar Katsina, an sayi buhun Shinkafar Bature N68-69,000 a wannan makon, yayin da a makon jiya aka saya N62,000, an samu karin N7000 kenan kan farashin makon jiya.
An sayi shinkafar Bature N71,000 a kasuwar Mile 12 International Market da ke jihar Legos a satin nan, yayin da a makon jiya aka sai da N65,000.
Ita ma dai kasuwar Kashere da ke jihar Gombe N75,000 ake sai da buhun a makon nan da ke shirin karewa, bayan da aka saya N65,000 a makon da ya gabata, hakan ke nuni da cewa an samu karin N10,000 kenan a mako ɗaya .
N73,000 aka sayi buhun Shinkafa 'yar waje a kasuwar Zamani da ke jihar Adamawa a satin nan, inda a makon da ya shude aka saya N55,000.
To bari ƙarƙare farashin shinkafar na wannan makon da kasuwar Giwa na jihar Kaduna, an sayar da buhun shinkafar waje N68,000 a satin nan, amma a satin da da ya wuce N65,000 ake sai da buhun.
Ga ma'abota cin alala da kosai kuwa, wake fari ya fi tsada a kasuwar Mile 12 International Market da ke jihar Legos, da aka sai da N130,000
Sai kasuwar Dawanau a jihar Kano a arewacin kasar, inda aka sayar da buhun N113-120,000 a kasuwar.
A Mai'adua jihar Katsina kuwa, an sayi buhun farin waken N117,000 a makon nan.
Da DCL HAUSA ta yi tattaki zuwa kasuwannin jihohin Gombe da Kaduna, ta taras da cewa ana sayen buhun farin waken kan kudi N107,0000 a kasuwar Giwa ta jihar Kaduna da kuma kasuwar Kashere da ke jihar Gombe.
Sai dai waken ya fi sauki a kasuwar Gombi da ke jihar Adamawa a wannan makon da aka sayar N90-95,000.
Bari mu kammala Farashin kayakin abinci na satin nan da farashin Kwalin taliyar Spaghetti.
A wannan makon da ke mana ban kwana dai, taliyar ta fi tsada a kasuwar Mai'adua jihar Katsina da sayar da kwalin N14,500, bayan da makon da ya shude aka saya N13,700.
Haka nan a wannan makon ma kudin kwalin taliyar N14,000 ne a kasuwannin jihohin Gombe da Kaduna, hakan kuwa aka sai da a makon da ya gabata ma.
A kasuwar Zamani da ke jihar Adamawa an sayi kwalin taliyar N13,500 a makon nan, yayin da a makon jiya aka sai da kan kudi N13,000, cif cif.
N13,500 ake sai da kwalin taliya a kasuwar Mile 12 International Market da ke jihar Legas a makon nan, haka zancen yake a makon da ya gabata.
A kasuwar Dawanau da ke Jihar Kano N14,000 ake sayar da kwalin taliyar a makon da ya gabata, yayin da a wannan makon da ke dab da ƙarewa ake sayarwa kan kudi N13,000, an samu ragin N1000 guda kan farashin makon da ya gabata.
DCL HAUSA A'isha Usman Gebi.