Tinubu zai dawo Najeriya bayan kwashe kwanaki a Turai


Fadar shugaban kasar Najeriya ta bayyana cewa shugaba Tinubu da mukarrabansa za su dawo Najeriya daga Turai a gobe Laraba.

Mashawarci na musamman kan bayanai da dabaru ga shugaban kasar Bayo Onanuga ne ya sanar a cikin wani sakon da ya wallafa a shafinsa na X yau Talata.

Indai za'a iya tunawa a ranar 22 ga Afrilu, Shugaba Tinubu ya bar Abuja zuwa kasar Netherlands a wata ziyarar aiki da yakai.

Post a Comment

Previous Post Next Post