Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya rattaba hannu kan dokar tantance lafiyar masu son yin aure.
A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnatin, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, ya ce dokar na nufin daga yanzu babu wani aure da za a ɗaura shi a Kano ba tare da gabatar da sakamakon gwajin lafiya ba.
Hakan na nufin rage yiwuwar haihuwar yara masu wasu matsalolin kiwon lafiya kamar sikila, cutar kanjamau da ciwon hanta.