Jihar Katsina na duba yiwuwar fara daukar mata a kwalejinta ta horar da kwallo

Kwalejin horar da kwallon kafa ta jihar Katsina za ta fara daukar mata don horar da su kwallon kafa a Kwalejin don yin adalci ga kowane bangare.

Sai dai, Kwalejin kamar yadda gidan talabijin na Channels ya rawaito, hakan zai yiwu muddin dama ta ba da.

Kwamishinan wasanni na jihar Katsina Zakari Shargalle ya sanar da hakan a taron manema labarai a Katsina, a lokacin da ya karbi bakuncin shugaban hukumar kwallon kafa ta kasa NFF Shariff Abdallah a lokacin da ya je Katsina don duba lamurran wannan sabuwar Kwalejin horar da kwallon kafa.

Zakari Shargalle ya ce kwallon kafa ta zamo sana'a mai kyau da duniya ke kallon akwai mafita a cikinta.

Ya ba da tabbacin cewa za a rika horar da 'yan wasa yadda ya dace da kuma shiga a fita don sanya su murza leda a kulob-kulob din kasa har ma da na kasashen ketare hade da tallafin hukumar NFF.

Post a Comment

Previous Post Next Post