Kwankwaso |
APC ta zargi dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP a zaben 2023, Engr. Rabiu Kwankwaso da kitsa zagon kasa ga shugaban jam'iyyar APC na kasa, Abdullahi Ganduje, gabanin zaben 2027.
Mai baiwa jam’iyyar APC shawara kan harkokin shari’a Farfesa Abdulkarim Kana ne ya yi wannan zargin yayin wata hira da gidan talabijin na Channels.
Abdulkarim yace shugabannin jam’iyyar NNPP na jihar Kano ke shirya zanga-zangar neman tsige Ganduje daga mukaminsa.