SERAP ta ba wa gwamnatin tarayya wa'adin sa'o'i 48 ta janye harajin CBN na 0.5%


Ƙungiyar kare hakkokin tattalin arziki ya yi gargadi ga Gwamnatin Tarayya da ta janye harajin kashi 0.5 cikin 100 da babban bankin Nijeriya CBN ya umurci bankunan 'yan kasuwa da su rika cire wani kason kudi daga kwastominsu don samar da tsaro ga harkokin intanet.

SERAP ta kuma yi barazanar daukar matakin shari'a a kan gwamnati idan har bata janye harajin cikin wa'adin sa'o'i 48 da ta bada.

Kungiyar ta sanar da hakan ne a ranar Talata a shafinta na X, inda ta yi kira da a gaggauta janye lamarin.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp