'Yan bindiga sunyi awon gaba da dalibai a jami'ar kimiyya da fasa a Kogi.

 'Yan bindiga sunyi awon gaba da dalibai a jami'ar kimiyya da fasa a Kogi.

A ranar Alhamis da daddare ne ‘yan bindiga suka kai hari Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Confluence (CUSTEC), Osara, Okene a Kogi, suka yi awon gaba da wasu dalibai.


Wani shaidar gani da ido ya ce ‘yan bindigar sun kai farmaki jami’ar ne da misalin karfe 9:00 na dare. yayin da daliban ke karatun jarabawar da za su yi.


Wata majiya ta ce ‘yan bindigan sun shigo ta cikin daji ne, suka shiga dakunan karatu uku, suka fara harbin iska.


Sun kama daliban a cikin zauren karatun, suka fara daukar su,makarantar ta shiga cikin rudani, yayin da daliban da suka firgita a wasu dakuna suka yi ta tururuwa, ta bangarori daban-daban a cikin makarantar.


A lokacin da jami’an tsaro na cikin gida da jami’an tsaro na yau da kullun da ke bakin kofar suka shigo  barayin, tuni suka yi nasarar sace wasu dalibai. Amma kokarin da jami'an su ka yi ya rage barnar da aka yi saboda maharan ba su wuce dakunan farko guda uku ba,


A cewar majiyar, daliban na shirye-shiryen jarabawar semester ta farko da ake sa ran za a fara a ranar Litinin 13 ga watan Mayu, lokacin da ‘yan bindigar suka far musu.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp