Kungiyar ƙwadago ta kudiri aniyar yin zanga-zanga ranar 12 ga watannan na Mayu idan ba'a janye batun karin kuɗin lantarki ba

 Kungiyar ƙwadago ta kudiri aniyar yin zanga-zanga ranar 12 ga watannan na Mayu idan ba'a janye batun karin kuɗin lantarki ba

Kungiyoyin kwadago a karkashin inuwar kungiyar kwadago ta Nijeriya NLC da (TUC) sun rubuta wasikar zanga-zanga zuwa hedikwatar hukumar kula da wutar lantarki ta kasa NERC.


Kungiyar, a cikin wasikar, wacce ke da hadin gwiwar shugaban kungiyar NLC, Comrade Joe Ajaero da shugaban TUC, Comrade Festus Osifo, hadi da sunayen sakataren gwamnatin tarayya (SGF), ministan kwadago da samar da ayyukan yi ta tarayya! Ministan wutar lantarki na tarayya da kamfanonin rarraba wutar lantarki (DISCOs), sun ba da wa'adin ranar 12 ga Mayu, 2024 cewa, NERC ta sauya daga maganar karin kudin wutar lantarki a Nijeriya.


Kungiyoyin biyu sun ba da misali da mawuyacin halin da karin kudin zai tura talakawa a matsayin dalilin kiran a koma baya.


Wasikar ta ce mun yi imanin cewa wannan matakin ba wai kawai abin zargi ba ne idan aka yi la’akari da matsalolin da ‘yan Nijeriya ke fuskanta a halin yanzu,

hakan yasa ba za mu zura ido ba, domin ana cin zarafin talakawa da ma’aikata irin wannan abin da ba za a amince da shi ba.


Wannan dalilin yasa muka rubuta wannan takardar domin ankarar da hukuma cewa muddin ba a janye wannan mataki ba,munshirya tsaf domin gabatar da wannan Zanga-zangar.

Post a Comment

Previous Post Next Post