Kwastam za su tsaurara bincike don kamawa tare da hukunta wadanda suka yi sanadiyyar mutuwar jami'insu a Katsina

Babban kwantrolan hukumar kwastam ta kasa Bashir Adewale Adeniyi ya yi fatar cewa za su yi duk mai yiwuwa don ganin kama tare da hukunta wadanda suka kashe jami'insu Auwal Haruna a jihar Katsina.

Bashir Adewale Adeniyi a lokacin da wata tawaga ta musamman ta ziyarci garin marigayin Kayawa na karamar hukumar Dutsi a jihar domin ziyarar ta'aziyya, ya ce ba za su yi kasa a guiwa ba wajen bin diddigi don gano wadanda suka yi wannan aika-aikar dom su ma su girbi abin da suka shuka.

Auwal Haruna dai, jami'in kwastam ya rasa ransa a lokacin da wasu gungun mutane da ake kyautata zaton 'yan sumogal ne suka farmake shi a lokacin da ya ke bakin aiki a kauyen Gamjin Makaho kan titin Katsina zuwa Dankama a karamar hukumar Kaita ta jihar a ranar 17 ga watan Afrilu, 2024.

Bashir Adewale da ya samu wakilcin babbar tawagar karkashin jagorancin kwantrolan hukumar kwastam mai kula da jihar Katsina, Muhammad Umar, ya ce tuni hukumar ta fara gudanar da bincike don gano wadanda suka aikata wannan lamari, har ma ya tabbatar da cewa idan aka gano su, to kuwa sai sun girbi abin da suka shuka.

Tawagar bayan ta'aziyya ga iyaye da sauran al'ummar garin Kayawa, sai da suka ziyarci makabartar da aka binne Auwal Haruna, inda suka yi masa addu'o'i na neman Allah Ya gafarta masa.

Wannan tawagar da ta hada kwantrolan hukumar da ke kula da shiyyar ta 4 wato FOU Zone 4, da mai kula da simtirim kan iyakar kasa ta Joint Boarder Patrol Team, sun ziyarci Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umar Radda, inda suka gabatar masa da ta'aziyyar babban kwantrolan hukumar na kasa bisa wannan rashi na ma'aikacinsu da suka yi. Kazalika, sun kuma ziyarci Mai Martaba Sarkin Daura Alhaji Umar Faruq Umar a fadarsa, shi ma suka yi masa ta'aziyyar wannan rashi da aka yi ma Auwal Haruna da ya rasu a lokacin da ya ke kokarin kare martabar kasarsa.

Post a Comment

Previous Post Next Post