Kasar Bénin ta sanar da toshe damar fitar da danyen man fetur din daga tashar jirgin ruwan ta zuwa kasuwannin duniya
Kafar yada labaran gidan radiyon France Internationale (Rfi) ne dai ya tabbatar da hakan
A wata Aprilun da ya gabata nan ne dai hukumomin mulkin sojan Nijar din suka sanar da fara tura danyen man din kasar daga cibiyar sa ta Agadem zuwa tashar ruwan ta Seme ta hanyar bututun da aka gina da zummar fitar da danyen man Nijar din zuwa kasuwannin duniya da ya har ganga dubu 90 a ko wace rana
Sai dai wasu na ganin kasar ta Bénin ta dauki wannan mataki domin maidawa kura aniyarta sakamakon matakin Nijar na cigaba da kin bude iyakar ta da Bénin din duk kuwa da umarnin bude tasu bodar da Shugaba Patrice Talon ya bada tun bayan matakin kungiyar ECOWAS na cire wa kasar ta Nijar takunkumin da aka kakaba mata