Ci-gaban Nijeriya ne gaban Shugaba Tinubu, ba soki-burutsun Atiku Abubakar ba - Fadar shugaban kasaFadar shugaban Nijeriya ta yi martani ga tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar game da kalamansa da ya yi a 'yan kwanakin nan.

A cikin wata sanarwa da Bayo Onanuga babban mataimaki na musamman ga shugaban kasar kan sadarwa da tsare-tsare ya fitar, ta ce dan takarar shugabancin Nijeriya a jam'iyyar PDP Atiku dama ya yi kaurin suna wajen kokarin bata suna da ba da bayanai masu rikitarwa don ya cimma wata manufa ta kashin kansa musamman don goga kashin kaji ga gwamnati mai ci.

Fadar shugaban kasar ta ce a cikin wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai na baya-bayan nan, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP da ya sha kaye ya yi kakkausar suka kan batutuwa da dama da ya kamata a gyara domin kada a yaudari jama’a wajen amincewa da karya a matsayin gaskiya.

Sanarwar ta ce gwamnatin shugaba Bola Tinubu ta yi amannar cewa duk wani dan Nijeriya mai kishin kasa na hakika, ba tare da la’akari da bambancin siyasa ba, ya kamata ya yi kokarin inganta hadin kan kasa da walwalar tattalin arzikin kasa, ba tare da nakasa hakikanin kokarin gwamnatin tarayya na karfafa zuba jari na cikin gida da waje ba.

Fadar shugaban kasar ta ce sabanin ikirarin na Atiku Abubakar, gwamnatin Shugaba Tinubu, a cikin shekara ta farko, ta samar da sama da Dala bilyan 20 a cikin tattalin arzikin ƙasar. Kazalika, yayin da shugaba Tinubu ke birnin New Delhi na kasar Indiya domin halartar taron kolin G20 a shekarar da ta gabata, shugabannin 'yan kasuwar Indiya sun zuba sabbin jari na sama da Dala bilyan 14.

Sanarwar Bayo Onanuga ta ci gaba tana cewa a yayin ziyarar da Shugaba Tinubu ya yi a kwanan nan zuwa kasar Netherlands, Firayim Minista, Mark Rutte, ya ba da sanarwar saka sabon saka hannun jari na Dala milyan 250 na 'yan kasuwar Holland a Nijeriya.

Kazalika, sanarwar ta ce bangarorin tattalin arziki daban-daban, musamman ta hanyar sadarwa, masana'antu, ma'adanai, mai da iskar gas, kasuwancin ta yanar guzo duk suna jawo sabbin hanyoyin zuba jari kai tsaye daga kasashen ketare.

Fadar shugaban Nijeriya ta ce ta ga abin mamaki ganin yadda Alhaji Atiku Abubakar zai iya zargin Shugaba Tinubu da rigima a kan ba da kwangilar gina babbar hanyar Lagos zuwa Calabar ga kamfanin Hitech Construction wanda ya ce mallakin gidan Chagoury ne saboda dan shugaban kasa, Seyi Tinubu, ya kasance cikin hukumar gudanarwar kamfanin, da ke garin Sagamu, jihar Ogun.

Sanarwar ta ce ya kamata ’yan Nijeriya, a yanzu, su saba da nuku-nuku irin na Atiku Abubakar a kan al’amuran kasa da dama. Sanarwar ta diga ayar tambaya, take cewa, shin ba abin mamaki ba ne a ce tsohon mataimakin shugaban kasar, mutumin da ya fito karara ya ce ya kafa kamfanin Intels Nigeria tare da wani dan kasuwa dan kasar Italiya a lokacin da ya ke aiki a Hukumar Kwastam ta Nijeriya, wanda hakan ya saba wa ka'idojin aikin gwamnati, a yanzu shi ne ke zargin wani?

Fadar shugaban kasa ta kara da cewa a lokacin da ya ke mataimakin Shugaban Nijeriya a tsakanin 1999-2007, ya ci gaba da huldar kasuwancinsa da Intels wanda ya yi manyan kwangiloli.

Sanarwar da Bayo Onanuga ya fitar din ta fito karara ta nuna cewa yana da kyau a bayyana a fili cewa Seyi Tinubu matashi ne dan shekara 38 wanda ke da ‘yancin yin kasuwanci a Nijeriya da kuma ko’ina a duniya bisa tsarin da doka ta tanadar. Kasancewar mahaifinsa a yanzu shi ne Shugaban Nijeriya bai hana Seyi ci gaba da harkokin kasuwanci na halal ba.

Post a Comment

Previous Post Next Post