Muhimman bayanai kan shugaban kasar Iran, Marigayi Raisi

 

An nada mataimakin shugaban kasa Mohammad Mokhber a matsayin shugaban riko na Iran bayan tabbatar da mutuwar Shugaba Raisi a hatsarin jirgin sama


Dan shekaru 63, Ibrahim Raisi ya mutu ne a yayin da ake tsaka da yaki tsakanin Isra’ila da Falasdinawa da gwamnatin Raisin ta Iran ke goya wa baya.  Ya shafe kusan shekaru uku yana shugabancin kasar, kuma ya bayyana aniyarsa ta sake tsayawa takarar shugabancin kasar a shekara mai zuwa.


Tsohon babban alkalin alkalan kasar ne.  Raisi ne ya maye gurbin Ayatollah Ali Khamenei, shugaban majalisar koli ta addinin Musulunci a Iran mai shekaru 85.


An haifi Raisi ne a garin Mashhad da ke arewa maso gabashin Iran, cibiyar addini ta mabiya Mazhabar Shi'a. Ya yi karatun addini kuma ya samu horo a makarantar hauza da ke birnin Qum, inda ya yi karatu a gaban manya-manyan malamai ciki har da Khamenei.


Haka nan kamar Ayatollah, shi ma Raisi na amfani da bakin yadi domin yin rawani, wanda ke nuna cewa shi sayyidi ne – zuriyar Annabi Muhammadu, matsayi mai mahimmanci a tsakanin musulmi.


Raisi ya samu gogewa a matsayinsa na mai gabatar da kara a yankuna da dama kafin ya zo Tehran a shekara ta 1985. A babban birnin kasar ne a cewar kungiyoyin kare hakkin bil'adama, ya kasance cikin kwamitin alkalai da ke kula da zartas da hukuncin kisa kan fursunonin siyasa, abin da ya sa wasu suka yi masa da lakabi da Mahaucin Iran.


Marigayi shugaban kasar na Iran ya dade yana cikin majalisar kwararru, hukumar da ke da alhakin zabar wanda zai maye gurbin shugaban kasa idan ya rasu.


Raisi ya zama shugaban kasar Iran a shekara ta 2021 a cikin karancin fitowar masu jefa kuri'a da kuma rashin cancantar 'yan takara masu neman sauyi da masu matsakaicin ra'ayi, kuma da alama ya samu kwakkwarar madogara ta sake zabe.


Kamar sauran manyan jami'an Iran, mafi munin kalamansa ya kebanta ga Isra'ila da Amurka, sai kuma kawayensu turawan Yamma.


Raisi ya yi jawabai da dama tun bayan fara yakin Gaza a watan Oktoba domin yin Allah wadai da kisan kare dangi da Isra'ila ke yi kan Falasdinawa, ya kuma yi kira ga kasashen duniya da su shiga tsakani.


Ya yi alkawarin daukar fansa kan Isra'ila bayan da ta yi wa ginin ofishin jakadancin Teheran da ke kasar Siriya hari tare da kashe 'yan kungiyar kare juyin juya halin Musulunci IRGC guda bakwai, ciki har da janar-janar guda biyu na soja.


Zaman makoki da jimami ake cigaba da yi a kasar Iran da wasu karin kasashen Musulmi bayan sanarwar da hukumomi suka fitar cewa Shugaban kasar Ebrahim Raisi ya mutu a wani jirgin sama mai saukar ungulu wato helikwafta dauke da shi da wasu jami'ai bayan da jirgin ya yi hadari a wani yanki mai tsaunuka da dazuzzukan kasar.


Hatsarin dai ya faru ne kamar yadda hukumominn kasar suka sanar ta dalilin rashin kyawun yanayi.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp