Ma'aikatan NiMet sun dakatar da yajin aikin da suka shirya shiga


kungiyoyin kwadago na hukumar hasashen yanayi ta Najeriya sun dakatar da yajin aikin da suka shirya shiga yau Litinin, 20 ga Mayu, 2024.

Hakan ya biyo bayan yarjejeniyar da aka cimma a jiya Lahadi a wani zama na musamman da kwamitin kula da harkokin sufurin jiragen sama da fasaha na majalisar wakilai tayi.

Yajin aikin dai na da nasaba da rashin cika masu alkawurra da gwamnati ta dauka.

Post a Comment

Previous Post Next Post