Jihar Zamfara za ta fara biyan mafi karancin llbashi N30,000 a watan yuni.

 Jihar Zamfara za ta fara biyan mafi karancin llbashi N30,000 a watan yuni.

Gwamnan jihar zamfara Dauda Lawal ya ce a watan yuni za a fara biyan mafi karancin albashi na N30,000 ga ma'aikatan jihar.

Ya bayyana hakan ne a yayin wata ganawa da shugabannin kungiyar kwadago reshen jihar Zamfara a Gusau.

Gwamnan yace aiwatar da mafi karancin albashi na N30,000 da nufin zaburar da ma’aikatan jihar da kara musu karfin gwiwa.

Ya bayyana wasu tsare-tsare daban-daban da gwamnati ta yi na inganta jin dadin ma’aikata, da suka hada da biyan albashin watanni uku da ba a basu ba, tallafin hutu, da sauran alawus-alawus.

Post a Comment

Previous Post Next Post