Gwamnan kano ya nemi a gina makarantar soji ta mata a Kano.

Gwamna ya nemi a gina makarantar soji ta mata a Kano.

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bukaci a kafa makarantar sakandare ta ‘yan mata ta sojojin sama a Kano domin karawa akan makarantar sakandaren maza da ke Kwa, karamar hukumar Dawakin Tofa, a kan hanyar Kano zuwa Katsina.


A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature ya fitar, Gwamna Abba ya yi wannan roko yayin ziyarar da shugaban hafsan sojin saman Nijeriya Air Vice Marshal Hassan Bala Abubakar ya kai gidan gwamnati a Kano.


Ya kuma nuna jin dadinsa a bisa kwarewa da kuma tarihin Air Marshal Abubakar, inda ya yaba da kokarin rundunar sojin saman kasar nan wajen magance kalubalen tsaro, musamman wajen yakar masu garkuwa da mutane, ‘yan fashi, da sauran masu aikata laifuka a Kano.


Gwamnan ya jaddada kudirin gwamnatinsa na tallafawa rundunar sojin sama da kuma ‘yan uwa jami’an tsaro, inda ya jaddada muhimmancin hadin kan su wajen wanzar da zaman lafiya a Kano da kasa baki daya.

 A nasa jawabin Air Vice Marsha Hassan Abubakar, ya nuna damuwarsa kan yadda ake ci gaba da yankad filin jirgin saman NAF da matsugunin sa, inda ya bukaci a maido da filin da aka sadaukar domin fadadawa nan gaba.


Ya kuma nemi goyon bayan Gwamna Abba wajen hada cibiyar samar da ruwan sha ta jihar Kano da na matsugunin sojojin sama domin inganta samar da ruwan sha a Jihar.

Post a Comment

Previous Post Next Post