Ana barazanar daina kai tumatir a kudancin Nijeriya daga arewa


Kungiyar dillalan tumatir da hadaddiyar kungiyar masu safarar kayan abinci da dabbobi ta Nijeriya, na barazanar daina kai tumatir a jihar Lagos. 

Hakan ya biyo bayan zargin wulakanta musu kaya da suka ce ana yi.

Alhaji Ahmad Alaramma, shugaban kungiyar dillalan tumatir din ne ya sanar da hakan a taron manema labarai da suka kira a Zaria jihar Kaduna.

Ya ce lamarin da ya faru a kasuwar Oke-Odo a jihar Lagos ya jaza an lalata musu 'kiret' kusan 60,000 na tumatir, saukin ma, babu tumatir din a ciki.

Ya ce ana sayar da kowane 'kiret' daya na tumatir a kan kudi N6,000, da yanzu haka mambobin kungiyar sun yi asarar kudin da suka kai N360m.

Post a Comment

Previous Post Next Post