'Yan bindiga sun yi mummunan ta'adi a Dan Musa jihar Katsina


Wasu mahara da tsakar daren Lahadin wayewar Litinin din nan, sun farmaki kauyen Mai Dabino na karamar hukumar Danmusa a jihar Katsina, inda suka hallaka wani mutum daya tare da sassara karin mutum daya.

Lamarin ya faru da misalin karfe 2:30am na dare wayewar Litinin, kamar yadda majiyar DCL Hausa ta tabbatar.

Bayanai sun ce mutumin da 'yan bindigar suka ji wa raunuka, sun sassare shi da wuka a idanu, da yanzu haka ana hanyar zuwa da shi Katsina don ceto ransa.

Kazalika, maharan sun kuma sace wata mata, inda suka nufi daji da ita da har lokacin hada wannan labarin ba a san halin da take ciki ba kuma ba su bugo waya don neman abin fansar ta ba.

Majiyar DCL Hausa ta ce maharan sun kuma barke wani shagon da ake cajin waya, inda suka saci wayoyi da cazoji da sauran kayan amfani a shagon.

Sannan kuma rahotanni sun ce 'yan bindigar sun kori dabbobi a garin da har yanzu ba a iya tantance adadinsu ba.

Majiyar ta ce mutanen garin sun zaci cewa jami'an sa kan Community Watch Corps ne a lokacin da suka ji karar harbe-harben bindiga, sai daga bisani suka farga cewa ashe 'yan bindiga ne.

Ya zuwa lokacin hada wannan labarin dai hukumomi ba su ce uffan ba game a da wannan lamari.

Kauyen Mai Dabino na daga cikin kauyukan karamar hukumar Danmusa da ke fama da matsalar tsaro, tare da kauyuka irinsu Dunya, Kaigar Malamai da sauransu.

Post a Comment

Previous Post Next Post