A wannan makon masara ta fi tsada a Kasuwar Mile 12 International Market da ke Legos da aka saida ₦65,000, yayin da a makon da ya gabata aka sayar ₦60,000 daidai, an samu karin ₦5000 a makon nan.
Sai kuma kasuwar Gombi da ke jihar Adamawa, inda a wannan makon aka sayi buhun Masarar ₦57-60,000, bayan da a makon jiya aka sayar ₦45-47,000.
A nan ma an samu karin kusan 13,000,a mako ɗaya kacal.
Ita ma dai Kasuwar Giwa da ke jihar Kaduna, ana sayar da Masara ₦57,000 a wannan makon da ke shirin karewa, amma a makon jiya ₦53,000 aka sai da buhun masarar.
To a kasuwar Mai'adua jihar Katsina kuma ₦58,000 kuɗin buhun yake a makon da ya wuce, sai dai a makon nan kuɗin buhun ₦62,000 ne, an samu karin 4000, kenan a kasuwar Mai'adua jihar Katsina a wannan mako.
Masara ta fi sauki a kasuwar Kashere da ke jihar Gombe sama da sauran kasuwannin kasar a wannan makon, inda aka sai da buhun masara ₦55,000, sai dai makon jiya ₦50,000 kuɗin buhun yake a Kasuwar.
Haka nan a kasuwar Dawanau da ke jihar Kano ma an samu karin 4000, kan farashin makon jiya da saida ₦54,000, amma a makon nan ₦58,000 kuɗin buhun yake a kasuwar.
Ita kuwa shinkafar Hausa ta fi tsada a kasuwar Kashere da ke karamar Hukumar Akko a jihar Gombe, da aka saida buhun ₦120-130,000, bayan da aka saya ₦105-115,000, a makon da ya wuce.
Amma a kasuwar Giwa da ke jihar Kaduna kuwa shinkafar Hausar ta ɗan sauka, an dai sai da buhun shinkafar ₦125,000 a makon jiya, yayin da a makon nan kuɗin buhun ya kama ₦120,000 cif, an samu ragowar ₦5000 kenan kan farashin na baya .
Shinkafar Hausar ta faɗi a kasuwar Girie da ke jihar Adamawa da aka sai da ₦110,000, bayan da a makon jiya aka sayar ₦125,000.
Da DCL HAUSA ta leka kasuwar Mile 12 International Market da ke Legos kuwa kuɗin buhun Shinkafar 'yar gida ₦120,000 ne a wannan makon, yayin da a makon jiya aka sai da ₦125,000.
Hakazalika a kasuwar Mai'adua jihar Katsina ma ₦120,000 aka sai da buhun shinkafar a makon nan,sai dai a makon jiya ₦105,000 aka sai da buhun, hakan na nuni cewa shinkafar ta haura a makon nan.
To a kasuwar Dawanau da ke jihar Kano an sayi shinkafar 113,000 a makon da ya gabata, amma a makon nan,₦118,000 aka sai da buhun, an samu karin ₦5000 kenan a makon nan da ke dab da ƙarewa.
Shinkafar waje kuwa ta fi sauki a wannan satin a kasuwar Zamani da ke jihar Adamawa, da ake sayarwa ₦55,000, bayan da makon da ya gabata aka sai da ₦70,000 daidai.
A jihar Gombe da ke makwabtaka da jihar Adamawa, an sayi shinkafa 'yar waje kan kuɗi ₦62-65,000
An samu karin ₦2000 kenan kan farashin makon da ya gabata da aka sai da ₦62-63,000.
₦65,000 ake sai da buhun shinkafar Bature a kasuwar Mile 12 International Market da ke Legos a makon da ya shude, haka nan farashin bai sauya zani ba a wannan makon.
A kasuwar Giwa da ke jihar Kaduna kuwa, an sayi buhun Shinkafar waje ₦68,000 a makon da ya kare, amma makon nan ₦65,000 kuɗin buhun Shinkafar.
Sai dai fa a kasuwar Mai'adua kudin Buhun shinkafar Bature bai canza zani ba a satin nan,inda ake sai da buhun₦62,000 haka batun yake a wannan makon.
To bari mu kammala Farashin Shinkafar Baturen da Kasuwar Dawanau a jihar Kano da ke Arewacin Najeriya,an sayi buhun Shinkafar waje ₦62,000 a makon jiya, sai dai a satin nan ₦71,000 aka sai da buhun, an samu karin kudi har ₦11,000 a mako guda kawai, wanda aka danganta hakan da tashin farashin CFA a kasar.
A bangaren Taliyar Spaghetti kuwa ta fi tsada a kasuwannin jihohin Kano da Kaduna, ina aka sayi kwalin taliyar ₦14,000 a kasuwar Dawanau a jihar Kano, hakan nan a kasuwar Giwa da ke jihar Kaduna ma ₦14,000 ne kuɗin Kwalin taliyar a makon nan,an samu karin dubu guda kenan kan farashin makon jiya a kasuwar giwa da ke jihar Kaduna, amma a kasuwar Dawanau kuwa₦13,500 ne ake sai da kwalin taliyar a makon jiya.
Kwalin taliyar ya fi sauki a kasuwar Zamani da ke jihar Adamawa da aka saya kan kuɗi ₦12,700 a makon nan,yayinda aka sayi kwalin ₦13,000 a makon daya shude,an samu sassaucin 300 kenan a kasuwar.
A Mai'adua jihar Katsina ₦13,700 ake saida kwalin taliyar a makon nan, amma a makon jiya ₦13,500 aka sai da, nan ma karin ₦200 kenan aka samu a satin nan.
Ita kasuwar Mile 12 International Market da ke Legos ana sayar da kwalin taliyar ₦13,000 cif, bayan da a makon daya kare aka sayar ₦13,500.
A karshe sai kasuwar Kashere dake jihar Gombe, an sayi kwalin taliyar kan kuɗi ₦12,600 a makon nan, hakan batun yake a makon da ya kare.
DCL HAUSA A'isha Usman Gebi.