Zargin cin hanci da rashawa:An dakatar da Shugaban Jam'iyyar APC na Kasa.

 Zargin cin hanci da rashawa:An dakatar da Shugaban Jam'iyyar APC na Kasa.

Jam’iyyar APC reshen mazabar Ganduje dake karamar hukumar Dawakin Tofa, jihar kano, ta dakatar da shugaban jam’iyyar na kasa Dr. Abdullahi Umar Ganduje.Mai bai wa jam’iyyar shawara kan harkokin shari’a na mazabar Ganduje Halliru Gwanzo shi ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Kano.


Halliru Gwanzo ya ce sun yanke shawarar dakatar da Dakta Ganduje daga jam’iyyar ne saboda zargin karbar cin hanci da gwamnatin Kano ke yi masa.


Sun ce dakatarwar ta fara ne yau 15 ga Afrilu 2024.

Post a Comment

Previous Post Next Post