Hukumar EFCC ta tabbatar da kwato N32.7billion da $445,000 daga ma'aikatar jin kai ta kasa.

 Hukumar EFCC ta tabbatar da kwato N32.7billion da $445,000 daga ma'aikatar jin kai ta kasa.Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ta tabbatar da kwato naira biliyan 32.7 da kuma dala 445,000 yayin binciken jami’an ma’aikatar jin kai da kula da walwalar al'umma na baya da na yanzu.


Jaridar DAILY NIGERIAN ta ruwaito cewa, a ranar 8 ga watan Janairu, shugaban kasa, Bola Tinubu, ya dakatar da ministar harkokin jin kai, yaki da ci gaban al’umma, Betta Edu, kan badakalar kudade.


Betta Edu dai ta fuskanci suka ne bayan da wata takarda ta bayyana a yanar gizo, inda ta bukaci babban akanta na tarayya Oluwatoyin Madein da ta tura kudi naira miliyan 585 zuwa wani asusu mai zaman kansa.


Ajuri Ngelale, mai magana da yawun shugaban kasa, ya ce Mista Tinubu ya umurci hukumar yaki da yiwa tattalin arzikin Kasa ta’annati, EFCC, ta gudanar da cikakken bincike a kan dukkan al’amuran da suka shafi hada-hadar kudi da ta shafi ma’aikatar da Edu ke jagoranta.


A baya-bayan nan dai an samu rahotannin da ke nuna cewa hukumar EFCC ta kwato sama da Naira biliyan 30 daga hannun  Edu, wanda daga baya ta musanta.


Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ce binciken da takeyi ya shafi jami'an ma'aikatar na da da na yanzu.

Post a Comment

Previous Post Next Post