Jami'an tsaro sun ceto sauran daliban jami'ar Gwamnatin tarayya ta Gusau su 23 da karin wasu masu yiwa kasa hidima (NYSC).

 Jami'an tsaro sun ceto sauran daliban jami'ar Gwamnatin tarayya ta Gusau su 23 da karin wasu masu yiwa kasa hidima (NYSC).


Ragowar ma’aikatan Jami’ar tarayya da ke Gusau a Jihar Zamfara da aka sace a ranar 22 ga Satumba, 2023, sun samu ‘yanci.


Wasu ‘yan bindiga a kwanakin baya sun kai farmaki gidajen kwanan dalibai a unguwar Sabon-Gida da ke karamar hukumar Bungudu a jihar Zamfara, inda suka yi awon gaba da dalibai sama da 20,da yawancinsu mata ne.


Bayan kokarin da hukumomin jami'ar da 'yan uwan su suka yi, an sako wasu daga cikin wadanda aka kama bayan watanni, amma 23 sun ci gaba da kasancewa a hannunsu 'yan bindingar.


Sai dai wata majiya ta shaida wa Daily Trust cewa jami’an tsaro sun ceto sauran daliban a ranar Lahadin da ta gabata.


An sako su ne a Kuncin Kalgo da ke karamar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara kuma aka mika su ga jami’an gwamnati ranar Lahadi. Jimillar mutane 23 ne gaba daya,kamar yadda wata majiya ta bayyana



Majiyar ta kara da cewa an kubutar da wasu daga cikin masu yi wa kasa hidima (NYSC) da aka sace a jihar Sokoto.


Jihar Zamfara dai na daya daga cikin jihohin da rikicin ya shafa a yakin da ake yi da ‘yan bindigar da suka addabi mazauna yankin Arewa maso yamma.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp