Har yanzu ba mu ga darajar da Naira ta samu kan Dala ba a kasuwa, don farashi ya ki sauka in ji 'yan Nijeriya

 Har yanzu ba mu ga darajar da Naira ta samu kan Dala ba a kasuwa, don farashi ya ki sauka in ji 'yan Nijeriya





‘Yan Nijeriya sun koka da cewa duk da farfadowar darajar Naira a kan kudaden kasashen waje a ‘yan kwanakin nan, farashin kayayyakin abinci da na kayayyakin masarufi bai sauka ba.


Sun bayyana hakane a wani bincike da Daily Trust ta gudanar a shafukan sada zumunta, inda suka ce zuwa yanzu babu abinda yafaru a kwanakin nan.


Daily Trust ta ruwaito cewa Naira ta samu gagarumar nasara a ‘yan kwanakin nan biyo bayan kakkausar murya da babban bankin ƙasar ya yi na kare kudin gida a kan dala.


Dalar dai da ta kusa kaiwa N2,000 makwanni da suka gabata, zuwa yanzu takoma kusan Naira 1,150 a kasuwar da ke bayan fage


A lokacin da Naira ke fama da faduwa, farashin kayan abinci da kayayyakin da ake shigowa da su daga waje sun yi tsada sossai, lamarin da ya kara tabarbare tsadar rayuwa a Nijeriya.


Daily Trust ta tattauna da wasu yan Nijeriya inda suka cigaba da bayyana ra'ayoyinsu game da yadda naira take kara daraja amma haryanzu kayan masarufi basuyi sauki ba


Sedai duk da haka, sun yi fatan abubuwa za su fara sauka idan gwamnati ta ci gaba da tafiyar da yadda harkar kudade a halin yanzu.

Post a Comment

Previous Post Next Post