Karamar hukumar Danmusa na bukatar daukin gaggawa a bangaren tsaro in ji Danmusa Forum

Kungiyar tabbatar da shugabanci na gari ta karamar hukumar Danmusa wato (Danmusa LG Forum for Good Governnace) ta roki gwamnatin jiha da ta samar da shingen jami'an tsaro akan hanyar Yantumaki zuwa Danmusa don tababbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al'umma. 

Shugaban kungiyar kwamarad Haruna Jafaru Danmusa ya yi wannan rokon a cikin wata sanarwa da ya fitar aka kuma raba wa manema labarai a Katsina. 

Kamar yadda ya ce hanyar Yantumaki zuwa Danmusa ta kasance cikin hatsari a halin yanzu sakamakon yawan hare-haren da 'yan bindiga ke kai wa matafiya a hanyar wanda ke jawo rasa rayuka da kuma yin garkuwa da mutane.

Ya kara da cewa 'yan ta'adda sun mayar da hanyar abin tsoro ga jama'ar yankin sakamakon yadda kusan duk rana ta Allah sai sun tare matafiya a hanyar.

Kwamarad Haruna jafar ya jaddada cewa kiran ya zama wajibi ta la'akari da yadda hare-haren 'yan ta'adda ya kassara tattalin arzikin al'ummar yan'kin. 

Shugaban kungiyar ya yi amfani da damar wajen yaba ma gwamnatin jiha bisa irin kokarin da ta ke yi wajen tabbatar da kawar da matsalar tsaro a fadin jihar.

Post a Comment

Previous Post Next Post