'Yan Bindiga sun hari garin Maradun na jihar Zamfara

'Yan Bindiga sun kai hari garin Maradun na jihar Zamfara inda Sun halaka mutanen 2, tare da sace,mutum 30.

https://drive.google.com/uc?export=view&id=11jdk7ctr5oP_oQDsKoQGfyYolgZZsedX

Mazauna garin Maradun, mahaifar karamin ministan tsaro, Bello Matawalle, sun shiga cikin zullumi yayin da wasu ‘yan bindiga suka mamaye garin da safiyar Juma’a.

Rahotanni sun bayyana  cewa ‘yan bindigar sun kai hari garin ne da misalin karfe 2:00 na dare kuma an kwashe kusan sa’o’i biyu ana harbe-harbe tare da lalata  gidajen mutane.


LEADERSHIP ta rawaito cewa, duk da cewa har yanzu ba a tantance ainihin adadin mutanen da aka sace ba a lokacin harin, amma adadin ya kai kusan 30 da suka hada da mata da yara da manya idan aka yi la’akari da adadin gidajen da abin ya shafa.

Wani basaraken gargajiya da ‘yan fashin suka yi wa gidan sa kawanya ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda matsalar tsaro ke karuwa a garin.

Post a Comment

Previous Post Next Post