Watanni 11 bayan cire tallafin man fetur 'yan Nijeriya har yanzu na fuskantar karancin man fetur, tare da gama da dogayen layi.
Watanni 11 bayan da gwamnatin tarayya ta cire tallafin man fetur ‘yan Nijeriya na ci gaba da kokawa kan halin da ake ciki na karancin man fetur da dogayen layukan da ake samu a gidajen mai a fadin kasar.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ‘yan kasuwar man fetur suka yi ta zargin karancin man fetur da ake fama da shi a halin yanzu yayin da ake ci gaba da samun layukan man fetur a manyan biranen kasar nan duk da tabbacin da Kamfanin mai na Nijeriya (NNPCL) ya bayar na cewa ana samar da man a kai a kai.
Shugaba Bola Tinubu ya cire tallafin man fetur gaba daya a ranar 29 ga watan Mayun 2023 a lokacin rantsar da shi, kuma farashin man fetur ya yi tashin gwauron zabi a fadin kasar nan.
Wannan cire tallafin man fetur ya kamata ya bude kofar shigo da mai zuwa kamfanoni masu zaman kansu a matsayin wani bangare na tanadi a cikin dokar masana’antar mai ta 2021, don haka ya dauki nauyin shigo da mai daga NNPCL.
Sai dai kuma NNPCPL ya kwashe watanni da dama ya kuma zama shi kadai ke shigo da mai a Nijeriya, saboda kamfanonin mai masu zaman kansu ba sa iya samun kudaden kasashen waje don shigo da su daga kasashen waje.
A baya dai hukumar NNPCPL ta sanar da cewa ba ita kadai ce ke samar da albarkatun man fetur a kasar ba, amma lamarin ya sauya sakamakon karancin man fetir.