Rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da janye jami’an ta na hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Kano.

 Rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da janye jami’an ta na hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Kano.

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano,ta tabbatar da janye jami’anta daga hukumar sauraron korafe-korafen jama’a da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano (PCACC).


Rundunar ‘yan sandan a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai magana da yawunta, Abdulahi Haruna Kiyawa, ta ce janyewar jami’an ta na da nufin gudanar da bincike kan ma’aikatan da nufin gano ainihin adadin jami’an ‘yan sandan da hukumar ta amince da su tare da gano irin ayyukan da kowane dan sanda ke yi tun lokacin da aka tura shi hukumar a shekarar 2015.


Hakan ya biyo bayan rahotannin da aka samu ta sashin amsa korafe-korafe na rundunar ‘yan sanda (CRU), inda ke nuna ‘yan sandan da ke da alaka da hukumar a matsayin masu rike da madafun iko tare da kaucewa aikin da ake sa ran na samar da gadi da sauran ayyuka a hukumar.


Jama’a su lura cewa, abin da ake ci gaba da yi na ma’aikata shi ne magance yawan korafe-korafe kamar yadda wasu kafafen yada labarai suka ruwaito.


Daukar matakin ya zama wajibi, domin a gyara kura-kurai da ke fitowa fili a cikin ayyukan Hukumar kamar yadda aka fara amfani da Jami’an ‘yan sanda da aka tura zuwa gadi da sauran ayyuka wajen kamawa da gudanar da bincike a kan kararraki wanda a fili ya saba wa nasu na asali. wajabcin da aka sanya kuma dole ne a gyara.


Matakin shine tabbatar da ingancin aikin na ƴan sanda ba tare da cin zarafi don wani ko wata a cikin al'umma ba.

Post a Comment

Previous Post Next Post